An Gudanar Da Zaɓukan Fidda Gwani Na APC A Bakori, Faskari Da Dandume Da Ke Katsina.
An gudanar da zaɓukan fidda gwani na jam’iyar APC domin cike guraben yan takarar ƙananan hukumomi da na kamsiloli a shiyar Funtua.
Jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Katsina ne suka duba zaɓukan a shiyar.
A Danja, an gudanar da zaɓukan cikin kwanciyar hankali.
Alhaji Nura Rabi’u Dabai shi ne aka naɗa a matsayin shugaban kwamitin kula da zaɓen na jam’iyar ta APC, yayinda aka naɗa Habibu Sa’i a matsayin sakataren kwamitin.
Dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyar Funtua, Sanata Muntari Dandutse, mataimakin shugaban jam’iyar APC na shiyar Funtua Ibrahim Danjuma da kuma kwamishinan kula da harkokin addinai Isyaku Dabai sun duba yadda zaɓen ya gudana a ƙaramar hukumar Danja.
A jawabinsu jin kadan da kammala zaɓen, Muntari Dandutse, Isyaku Dabai da kuma Ibrahim Danjuma sun yaba ma wakilan masu zaɓe wanda suka gudanar da zaɓen tare da nuna halin dattaku.
A nashi ɓangaren, ɗan takarar jam’iyar na ƙaramar hukumar Danja Rabo Tambaya ya bayyana jin daɗi bisa samun nasarar gudanar da zaɓukan fidda gwanin cikin nasara.
Rabo Tambaya Danja ya bayyana hanyar da jam’iyar ta yi amfani da ita wajen gudanar da zaɓen ƴan takarar a matsayin wadda tafi dacewa don tabbatar da zaman lafiya a cikin jam’iyar.
Rabo Tambaya ya ce jam’iyar APC a ƙarƙashin shugabancin Dr. Dikko Umaru Radda ta yi abinda ya kamata don ciyar da jihar ta Katsina gaba.
Ya yaba ma gwamnan bisa ɗaukar ma matsalar tsaro a yankin matakai.
A tsokacinshi, shugaban Kwamitin kula da zaɓen Nura Rabi’u Dabai ya ce zaɓen nasara ce sosai.
A gudanar da zaɓukan a Bakori, Dandume da Faskari cikin nasara.
An zaɓi yan takarar na ƙananan hukumomi da kamsilolin ne ba tare da hamayya ba.
An bayyana Aminu Dan Hamida a matsayin wanda ya samu nasara zama ɗan takarar ƙaramar hukumar Bakori, Surajo Daudawa wanda ya samu nasara a Faskari, sai Bishir Gyazama wanda ya samu nasara a Dandume.
