‘Yan Bindiga Sun Kashe Manomi, Sun Sace Mutum 7 A Kaduna.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani ba kauye tare da yin garkuwa da wasu mutane bakwai – mata biyar da maza biyu a Unguwar Gajere da ke Kutemeshi a karamar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.
Harin ya rutsa da su ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu a ranar 2 ga watan Agusta, 2023, kamar yadda majiyoyin yankin suka bayyana.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kakangi a majalisar dokokin jihar Yahaya Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da dabbobi a wasu unguwannin da ke makwabtaka da su.
A cewarsa, lamarin yana da ban tsoro yayin da yake jajantawa iyalan wanda aka kashen.
Ya ce ‘yan ta’addan sun saba yin satar dabbobi a Gwandu da kauyen Damari, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.
