September 17, 2026

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sarakuna 2 A Imo.

0

Wasu ‘yan bindiga, a ranar Litinin din nan sun kashe wasu sarakunan gargajiya biyu a kananan hukumomin Aboh da Ezinihitte Mbaise na jihar Imo a lokacin da suka kai wasu hare-hare.

‘Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe basaraken Nguru, a karamar hukumar Aboh Mbaise, Eze Mmirioma, a lokacin da suka mamaye fadarsa kafin daga bisani su gudu da misalin karfe 3 na rana. Daga baya kuma ya ce ga garinku a asibitin Ndubuisi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Mohammed Ahmed Barde, ya tabbatar da faruwar harin tare da yin Allah wadai, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership ta bayyana.

A wani sako da kakakin rundunar ‘yan sandan Imo, Henry Okoye, ya fitar ya ce: “Kwamishanan ‘yan sandan jihar Imo, CP Mohammed Ahmed Barde psc ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Eze Mmirioma, basaraken gargajiya a Aboh Mbaise wanda ya rasu a lokacin da ake jinya a asibitin Ndubuisi bayan da wasu ‘yan bindiga suka harbe shi a gidansa a yau.”

Bugu da kari, ya ce an fara gudanar da bincike, inda ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda ya kafa wata babbar tawagar bincike don gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa an kama waɗanda suka aikata wannan danyen aiki tare da fuskantar fushin doka.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana sunan sarkin Ezinihitte ba, wanda majiyoyi suka ce an ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawa.

Jihar Imo dai na fuskantar hare-hare daban-daban tun bayan da aka fasa gidan kaso a Owerri da kuma fargabar da ake yi kan dokar zaman gida a shiyyar Kudu maso Gabas.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *