September 18, 2026

Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina Ta Gano Motocin Da Ake Zargin Na Sata Ne.

0

Daga Auwal Isah

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar gano mota kirar kanta da ake zargin ta sata ce mai lamba SKK 98 ZY da aka aje a unguwar Shinkafi, Katsina.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar SP Isah Gambo.

Saboda haka sanarwar ke buƙatar idan mai ita ya samu labari ya zo da takardun dake nuna tashi ce domin amsar abun shi.

Idan za a iya tunawa, an gurfanar da wani gungun mutane karkashin jagorancin Abba Kala da wani Muhammed Abdulrahaman da aka fi sani da LALO wanda ake zargin na yan fashi da makami ne. Gungun nada alaka da kyasa-kyasan fashi da makami da ake aikatawa a cikin birnin Katsina, inda kuma aka samu mota kirar Toyota Corolla a hannunsu.

A lokacin da ake ci gaba da bincike, an gano wata motar kirar Honda EOD da aka yima wani mutum mai suna Abdullahi Sani fashin ta a unguwar Kofar Marusa cikin garin Katsina da kuɗin ta ya kai naira miliyan 2.8 wadda mutanen da ake zargi suka sayar da ita a Makurdi cikin jihar Benue akan kuɗi naira N350,000, shima wanda ya saya ya saida ma wani mutum ita akan kuɗi naira miliyan N1.5m.

Hakan kuma, rundunar ta samu nasarar tarwatsa gungun wasu mutane da ake zargin yan fashi da makami ne dake matsa ma birnin Katsina bayan samun bayanan sirri a ranar 08/12/2022 da misalin karfe 02:30am.

Matanen da aka kama sun haɗa da wani mai suna Hamza Lawal da aka fi sani da “SHOW”, dan shekaru 25, Umar Adamu da aka fi sani da “JANKAI” dan shekaru 24 da haihuwa wanda suke unguwar Farin Yaro, Katsina.

Wannan mutanen dai an kama su ne a unguwar Yanturaku, Tudun Yanlihidda da buhunnan kebil din taransfoma 2, digga 1 mai tsini, wata digar ɗaya, zarton yankan karfe da kuma fitilun hannu masu haske.

A lokacin da ake gudanar da bincike, waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun haɗa kai da wasu kamar haka: Yau Ibrahim Hussaini da aka fi sani da Abba Kato, Abu Danta’aya da Dan’Audu Maimota inda suka saci kebil a stole a Alison Electric Store dake kan hanyar IBB Way, Katsina da kuɗin shi ya kai N503,000:00.

Idan dai za a iya tunawa, rundunar ta gabatar da gungun mutane a ranar 08/12/2022 da ake zargin sun kware wajen yima al’ummomin Katsina fashi, tare da amshe masu dukiya.

Lokacin ne rundunar ta sanar da neman Ibrahim Hussaini da aka fi sani da Kato dan shekaru 19 da haihuwa da ya gudu, wanda aka kama.

A shiyar Dutsinma karkashin jagorancin kwamandan rundunar na shiyar ta dakile wani hari, tare da kashe ɗan ta’adda 1, hadi da ceto wani da akai garkuwa da shi cikin koshin lafiya.

A ranar 12/2/2023 da misalin 04:45am ne ta samu kiran gaggawa cewa; yan ta’adda na harbin kan mai uwa da wabi da bindigu kirar AK47 a garin Kitibawa, karamar hukumar Dutsinma, tare da yin garkuwa da wani Alhaji Ado Rumawa mai shekaru 55 da haihuwa dake yankin.

Sannun rundunar ta dakile wasu yan fashi da makami dake amshe ma mutane kayan su akan hanyar Danja – Bakori, bisa mahadar Unguwan Balarabe karkashin jagorancin DPO mai kula da ƙaramar hukumar Danja.

A lokacin da ake duba wurin da lamarin ya faru, an samu gawar ɗaya daga cikin mutanen da ake zargin yan fashi ne, adda 1, wayoyin salula 3 da kuma sanda.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *