Hukumar NCC Ta Kama Mutanen Da Ake Zargin Yana Ma GOTV Da DSTV Kutse A Jihar Rivers.
Jami’an hukumar hana satar fasaha ta Najeriya sun samu nasarar kama wani da ake zargin yana yin aikin kutse ga kafafen watsa labarai zamani mai suna Mr. Ajaye West William.
Kamar yadda majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard ta bayyana, an kama shi ne bisa zargin aikata laifukan rarraba siginal din kamfanonin watsa labarai daban-daban, wanda ya saba wa dokar kare hakkin mallaka.
Jami’an hukumar ne suka bibiya tare da kama mtunen da ya gagara kamuwa a lokacin da suke ayukkan yaƙi da satar fasaha a Fatakwal da ke cikin jihar Rivers a karshen makon da ya gabata ya na cikin watsa siginal da na’urorinshi.
A cewar daraktan ofishin hukumar na Fatakwal Mr. Collins Nweke, aikin wanda aka gudanar tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro ya biyo bayan sa-ido da jami’an suka yi na tsawon watanni.
Ya bayyana cewa abubuwan da aka samu hannunshi sun hada da na’urorin kallo (decorder) na kamfanin DSTV, GOTV, Strong da FTA da kuma sauran kayan da ya ke yin amfani da su wajen rarraba siginal ga masu zuwa sayen katin da ke bada damar ayi kallo hannunshi.
A cewar Mr. Nweke, wanda ake zargin ya bada muhimman bayanai, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da nufin gurfanar da shi gaban kuliya. “An yi amannar cewa wanda ake zargin yana da abokan hulda ta hanyar watsa shirye-shirye ba bisa ka’ida ba, kuma hukumar tana bincike don gano tushen laifin,” in ji shi.
Kamen na baya-bayan nan ya biyo bayan gargadin da babban daraktan hukumar NCC, Dr. John O. Asein ya yi a kwanan baya a gidan talabijin na Channels, inda ya yi Allah wadai da dukkan nau’ikan satar fasaha.
“Duk wanda aka samu yana da hannu wajen rarraba siginal din watsa shirye-shirye da kuma wanda aka hada baki da su wajen aikata hakan, za a kama su a gurfanar da su a gaban kuliya, sannan kuma za a kwace kayan aikata laifin,” inji shi.
Babban daraktan ya bukaci jama’a da su kai rahoton irin wannan matsalolin ga ofishin hukumar mafi kusa.
Hukumar da ke kare hakkin mallaka ta Najeriya, NCC, ta kwace kayayyakin da suka kai sama da Naira miliyan 7, tare da wasu mutane bakwai da jami’an hukumar suka kama a yayin da suke gudanar da kama a yankunan Kubwa da Zuba a babban birnin tarayya, Abuja.
Hukumar kare hakkin mallaka ta Najeriya (NCC), ta ce ta gurfanar da wasu kararraki 31 a shekarar 2012, 26 daga cikinsu laifuka ne na ‘yan fashi da makami da kuma kararraki biyar.
