Muryar Talaka Ta Karrama Kanwan Katsina A Lokacin Taronta Na Shekara Shekara.
Kanwan Katsina hakimin Ketare ya yaba ma wata kungiyar daba ta gwamnati ba mai suna “Voice of the Masses” bisa shirya taronta na shekara shekara karo na 11.
Usman Bello Kankara na magane ne a matsayin uban taron da ya gudana a dakin taro na daukar ma’aikata ta jihar Katsina.
Basaraken ya yi kira ga kungiyar da ta maida hankali wurin wayar da kan al’umma ta hanyar radio don samun nasarar yin babban zaben shekarar 2023 dake tafe.
Usman Bello Kankara ya bukaci mutane da su tabbatar da cewa sun yi rijistar mallakar katin jefa kuri’a don ganin sun samu damar kada kuru’ar.
Kanwan Katsina ya ce ofishin gundumar ketare na aiki kafada da kafada da reshen kungiyar dake kamar hukumar Kankara wurin inganta walwalar al’umma, tare da bayyana cewa zai ci gaba da bada dama domin taimako ko bada shawarwari akowane lokaci ga kungiyoyin da bana gwamnati ba.
A lokacin taron, an mika ma Kawan Katsina hakimin Ketare Usman Bello Kankara lambar karramawa bisa rawar da yake takawa da kokarinshi ba gajiyawa wurin ganin an bunkasa rayuwar al’umma masu karamin karfi.
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Katsina Idris Usman Tune a wurin taron.
Sauran da suka hakarci taron sun hada shugaban kungiyar na kasa, dana jiha.
A lokacin taron Farfesa Usman Muhammad na jami’ar Abuja da Dr. Muktar Alkashim na jami’ar ABU Zaria, da dai sauransu sun gabatar da kasidu da bayanai.
Taken taron na wannan shekarar shi ne: yadda zaben shekarar 2023 zai tabbatar da dorewar demakaradiyya a Najeriya bayan kammala shi.
