September 18, 2026

Kungiyar Yan S-Power Ta Bukaci Masari Ya Maida Su Cikakkun Malamai.

0

Shugaban kungiyar malaman dake koyarwa a cikin shirin S-Power na jihar Katsina ya bukaci gwamnan jihar Katsina da ya maida malaman dake aiki a cikin shirin a matsayin cikakkin ma’aikatan gwamnati.

Comrade Sama’ila Rabi’u Musawa ya yi wannan rokon ne a lokacin da ya ke magana da yan jarida.

Kamar yadda ya bayyana, membobin kungiyar na aiki ka’in da na’in, kuma za su ci gaba da koyar da ilimin dake gare ga dalibai masu tasowa.

Comrade Sama’ila Rabi’u Musawa ya yaba ma gwamna ABM bisa kirkiro shirin S-Power a kokarinshi na farfado da bangaren ilimi.

Ya ce membobin kungiyar dake cikin shirin S-Power za su ci gaba da yaba ma gwamnan bisa maida su masu dogaro da kai.

Shugaban kungiyar ya kuma yaba ma gwamnan bisa gudanar da zaben fidda gwani lami lafiya.

Comrade Sama’ila Musawa ya yi kira ga gwamnatin dake tafe da ta duba yiyyuwar ci gaba da tafiyar da shirin na S-Power don bunkasa bangaren ilimi a jihar nan.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *