September 18, 2026

Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Yi Zargin Cewa Jami’an Tsaron Da Suka Buɗe Wuta a Kansa da Mabiyansa Sun Nemi Matarsa Ta Cire Kayanta.

0

Daga: Comrade Musa Garba Augie

Ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko.

Fiye da shekara shida ke nan tun bayan rikici tsakanin mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky da sojojin Najeriya, bisa zargin da sojoji suka yi na cewa mabiyansa sun tare musu hanya a Zaria.

Malamin ya ce wasu jami’an tsaro hudu dauke da makamai ne suka shiga karamin dakin da yake shi da iyalansa suka yi ta luguden wuta a shekarar 2015.

A cewarsa, jami’an tsaron sun kashe daruruwan mutane kafin su kai kansu kua suna “budewa [daki] suka gan mu suka ce ga wasu nan; ita matata..suka ce mata ta cire kayanta, da ta ce ba za ta cire ba suka ce a bude wuta.”

Ya kara da cewa bayan sun bude wuta ne dakin da suke ciki ya turnike da hayaki da kaurin harsasai.

“A lokacin akwai ‘ya’yana guda biyu a damana, ita kuma matata tana gabana sauran wasu ‘ya’yan nawa suna haguna. A takaice dai, nan take daya dan nawa mai shekara 15 suka harba masa harsashi ya shiga kokon kansa,” in ji Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Ya ce jami’an tsaron sun kashe ‘ya’yansa hudu- maza uku da mace daya baya ga ‘ya’yan riko da aka halaka a lokacin, yana mai cewa “sun dagargaza cinyata”.

Sheikh Ibrahim Zakzaky ya ce bayan kura ta lafa ne aka kai su asibitin sojoji daga bisani kuma aka sauya masa asibiti, yana mai cewa sai da ya yi wata uku yana jinya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *