September 18, 2026

Mai Ba Gwamnan Katsina Shawara Ya Bayyana Gaskiya A Matsayin Matakin Samun Nasara A Rayuwa.

0

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana jajircewa, kokari da kuma gaskiya a matsayin matakan samun nasara ga rayuwar dan adam.

Mai ba gwamnan jihar Katsina shawara akan ilimi mai zurfi Bishir Usman Ruwangodiya ya bayyana hakan a wurin walimar cin abincin dare da abokai da yan uwa suka shirya domin girmama Farfesa Yusuf Ibrahim El-Ladan bisa samun muƙamin Farfesa.

Tunda farko, saida makaddashin shugaban jami’ar Umar Musa Yar’adua dake nan Katsina Farfesa Abdulhamid Lawal wanda ya yaba da shirya walimar, ya lissafo matakan da ake bi domin samun muƙamin Farfesan.

Ya bayyana cewa jami’ar zata amfana da ilimin Yusuf Lawal El-Ladan ɗin.

Shima da yake magana, shugaban kwamitin tsare tsare wanda kuma shi ne shugaban sashen nazarin duniya da abubuwan dake cikin ta Dr. Abubakar Abdullahi wanda ya samu wakilcin Dr. Murtala Ruma ya bayyana wanda aka karraman a matsayin dattijo da jiha zata amfani da iliminshi.

A nashi bangaren, Farfesa Yusuf Ibrahim El-Ladan ya yi godiya ga @ SWA bisa samun damar taka muƙamin Farfesan.

A jawabansu na daban daban, yan uwa da abokai da suka haɗa da Dr. Babangida Ishaq Umar, Dr. Aminu Kalla Doro, Dr. Ibrahim Shu’aibu Safana, Engineer Muttaka Rabe Darma da kuma Hajiya Yaha Umma sun bayyana wanda aka karraman a matsayin mutum mai kokari da gaskiya, tare da yi mashi fatan samun nasara a rayuwarshi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *