Rabin Al’ummar Sabon Birnin Jihar Sokoto Na Jamhuriyar Nijar Saboda Matsalar Tsaro – Dan Majalisar Yankin.
Dan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltal yankin Sabon Birni na jihar Sokoto ya ce rabin al’ummar karamar hukumar na cikin jamhuriyar Nijar domin tsallake hare haren yan ta’adda.
Aminu Boza ya ce abun ƙaruwa ma yake yi a yankin na gabacin jihar Sokoton, inda ya kai ga shafar mutane kimanin dubu 50.
Ya bayyana hakan a lokacin da gidan radiyon DW ke zantawa da shi.
Dan majalisar ya ce babu wani tallafi da mutanen da abun ya shafa suke samu bayaga wanda jamhuriyar Nijar ke basu.
Wani mazaunin yankin ya ce kowace ranar duniya ta Allah da karfe 05:00pm ta yi sai mutanen yankunan su kama kwashe kayansu domin shiga jamhuriyyar Nijar su kwana don ganin sun tsallake tarkon yan bindiga zuwa gobe kuma su dawo domin ci gaba da hadahadarsu.
Saidai dukkan kokarin da aka yi na jin ta-bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Sokoto DSP Sanusi Abubakar bai yi nasara ba, saboda bai amsa kiran wayar salular da aka yi mashi ba.
Yanki dai ya yi sanu ta fannin kasuwancin kasa da kasa, inji Popular News Hausa.
