Masu Garkuwa Da Mutane Sun Kashe Wani Yaro Bayan Sun Karɓi Kuɗin Fansa Naira N2.5M a Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wasu Mutane uku da ake zargi da karbar kudin fansa N2.5m bayan kashe wani Yaro dan shekara shida da suka yi garkuwa da su.
Da yake jawabi ga manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar, Kakakin Rudunar ‘Yan Sandan jihar, Muhammed Shehu, ya ce wadanda ake zargin – Kabiru Idi, Danhauwa Kalla da Majami Iliya, sun yi garkuwa da Laminu Sani dan shekaru shida a Unguwar Bulunku cikin garin Gusau. kuma su bukaci a biya kudin fansa.Bayan sun karbi kudi fansa N2.5m, wadanda ake zargin basu saki yaron ba sai aka gano cewa an kashe shi.Inji Kakakin.
Kakakin Rudunar ‘Yan sanda ya Kara da cewa,, a ranar 3 ga Nuwamba, 2022, jami’an ‘yan sanda da ke aiki da sashin yaki da cin hanci da rashawa sun kama wadanda ake zargin suna da hannu wajen yin garkuwa da wani Yaro dan shekara shida, Laminu Sani, suka kamasu .
Kamun nasu ya biyo bayan korafin da wani Sani Garba ne ya kai wa ‘yan sanda cewa daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Kabiru Idi na kauyen “Yar katsina a karamar hukumar Bungudu ya yi hayar daki a gidansa kuma ya zauna na tsawon watanni uku.
A zamansa a gidan Idi ya hada baki da abokan aikinsa suka yi garkuwa da Yaron Garba, Laminu, da nufin karbar kudin fansa daga mahaifinsa.An ba su N2.5m, ba tare da sanin cewa sun riga sun kashe Yaron da suka sace ba.
“A yayin da ake gudanar da bincike, dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa tare da bayyana irin rawar da suka taka wajen sace Yaron.”
Kakakin Rudunar’ ‘Yan sanda ,Shehu ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin a yi musu shari’a.
