September 17, 2026

Yadda Muka Kama Wanda Ke Barazanar Satar Mutane Ta hanyar Aika Wasika A Katsina –‘Yan Sanda

0

Rundunar ‘yan sanda jihar |Katsina ta ce ta yi nasarar cika hannu da wani mai suna Muhammad Ibrahim dan shekaru 30 da ke kauyen Kagara a karamar hukumar Kafur da ke jihar Katsina bisa zargin yin bazarana zai sace wani mutun ko ya kashe ko kuma ya biya naira dubu dari.

Kakakin rundunar na jihar Katsina SP Gambo Isah ya bayyanawa manema labarai haka a Katsina a lokacin da yake kwalemar wasu makamai da ya ce sun yi nasarar kamawa a hannu ‘yan ta’ada a yakin da rundunar take yi na kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar Katsina

SP Gambo Isah ya kara da cewa wani mutun mai suna Bello Umar da ke garin Mahuta duk a cikin karamar hukumar Kafur a jihar Katsina ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda da ke Kafur cewa ya samu wata takarda da aka rubuta da hannu ana yi masa barazanar cewa ya biya kudi naira duba 100 ko a sace shi ko kuma ma a kashe shi.

“Wannan yasa ‘yan sanda ba su yi kasa a gwiwa ba suka bazama neman wanda ake zargin inda kuma suka yi nasararr damke shi, wanda yanzu haka yana hannu ana gudanar da bincike, sannan wanda ake zargin ya tabbatar da faruwar hakan.” Inji shi

Kakakin rundunar ‘yan Sanda ya kara da cewa yanzu haka ana cigaba da gudanar da binbike akan lamarin wanda ya ce da zaran an kammala za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya manta sabo.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *