Harkar Siyasa: Ya Kamata ‘Yan Fim Mu Mutunta Junanmu. Cewar Sa’idu Gwanja
.
Daga Mukhtar Yakubu
A daidai lokacin da harkokin siyasa suke ci gaba da kankama kamar kowanne rukunin mutane, su ma’ Yan fim ba a bar su a baya ba
to sai dai a wannan lokacin ana ganin sun fi samun rashin haɗin kai tare da rashin samar da Alkibla guda a tsakanin su.
Wannan ce ta sanya tsohon shugaban kungiyar masu shirya fim ta jihar Kano Alhaji Sa’idu Isa Gwanja ya yi kira a gare su, inda ya ce su haɗa kan su wajen gudanar da siyasar su ba tare da an samu sabani da juna ba.
A cikin wata tattaunawa da suka yi da wakilin mu, Sa’idu Isa Gwanja ya ce “Tun da Jam’iyyu sun kasance ba ɗaya ba, to ba zai yiwu a ce ra’ayin mutane ya zama iri ɗaya ba.
Don haka ya ce suma mutane ne kamar kowa, dole ne wani ya ji ya fi son waccan jam’iyyar wani ma ya ji ya fi son wata, kuma hakkin sa ne a matsayin sa na ɗan ƙasa ya yi abin da ra’ayin sa ne, sannan a dokar Masana’antar Kannywood kowa yana iya zaɓan abinda ya ke so.
“Amma dai abin da ya zama dole a tsakanin mu shi ne mu mutunta ra’ayin juna. Idan muka zo rigimar mu ta cikin gida ko abin da ya shafi sana’ar mu, sai mu yi kokari mu ga mun kare mutuncin junan mu, don haka muna so a kula a daina cin zarafin juna saboda ra’ayin siyasa, domin sana’ar mu daya ce” inji shi.
Kazalika ya ƙara da cewa, kada ra’ayin siyasa na dan wani lokaci ya haɗa mu faɗa da juna ta yadda ita siyasar ta ɗan wani lokaci ce, masana’antar Kannywood kuma tana nan da ita aka san su
Daga ƙarshe ya yi kira ga ‘Yan fim ɗin da cewar ya kamata duk wani ɗan takarar da za su yi, to su je masa da manufar su ta ciyar da masana’antar Kannywood gaba, domin duk wani abu da za su yi, idan sun gama siyasar Masana’antar za su dawo don haka su rinƙa yin siyasa don kishin Masana’antar su.
