Ni ban janye takara ba, har yanzu ina APC- Machina
Dan takarar kujerar sanata a shiyyar Yobe ta Arewa Bashir Sheriff Machina ya yi zargin wasu ne suka buga takardar bogin da ke cewa ya janye takararsa kuka ya ce fice daga jam’iyyar APC.
A cikin sanarwar da ofishin dan takarar ya aike wa wakilin DW Al-Amin Suleiman Mohammed, Machina ya ce ba shi da wata niyyar janye takara ko sauya sheka zuwa wata jam’iyya.
