September 19, 2026

Ana Binciken Wani Dan Sanda Saboda Yin Lalata Da Matashin Da Suka Tsare.

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu Ahmed Ammani ya bada umarnin gudanar da bincike kan wani jami’in dan sanda mai muƙamin ASP bisa zargin yin lalata da wani matashi da ke tsare a hannunsu, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.

Dan sandan na aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Awgu da ke jihar Enugu.

Umurnin binciken na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel ya fitar a Enugu wannan Asabar

Kwamishinan yan sandan jihar ya umarci sashen binciken manyan laifuka na jihar da ya gudanar da cikakken bincike, tare da gabatar da sakamakon da ya dace kan wannan zargi.

Ya bayyana cewa duk da an yi cin zarafin ne a ranar 18 ga Maris na shekarar 2022, dangin wanda aka tsare din mai shekaru 17 da haihuwa sun kawo koken ne kwanannan.

“Kwamishinan ya kuma ba da umarnin a kammala binciken cikin kankanin lokaci.

“Ya bada tabbacin cewa za a binciki koken yadda ya kamata, kuma dukkan wanda aka kama da laifi, za a hukunta shi yadda ya kamata,” in ji Ndukwe.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *