Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Ga Jami’an INEC a Enugu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da rajistar masu kada kuri’a a matakin mazaɓu a karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa jami’anta a ranar Laraba.
Kwamishinan INEC na kasa mai kula da sashen yada labarai da wayar da kan masu zabe, Barr. Festus Okoye ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce, sakataren hukumar INEC a jihar, Mista Jude Okwuonu ya ce da misalin karfe 2:30 na ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai wa jami’an hukumar dake gudanar da aikin rajistar masu kada kuri’a a makarantar Community Primary School Umuopu dake Umuozzi mazaɓu ta 19 dake karamar hukumar Igboeze ta Arewa.
Ya ce, “Yan bindigar sun yi ta harbe-harbe kan iska don tarwatsa masu rajista da jami’an dake aikin rijistar, tare da raunata daya daga cikin jami’ansu”.
Kamar yadda ya bayyana, an yi asarar na’urorin rijistar masu zabe guda biyu da sauran kayayyakin hukumar kamar wayoyin hannu.
Ya ce “Saboda haka, an dakatar da rajistar masu kada kuri’a a mazaɓar Igboeze ta arewa”.
Jaridar Vanguard ta ce a ranar 3 ga watan Yuli ne wasu da ba a san ko su waye ba suka kona ofishin INEC a karamar hukumar Igboeze ta Arewa.
“Duk da harin da aka kai ma hukumar ta samu nasarar ci gaba da yin rajistar a matakin mazabar, tare da taimakon ‘yan banga da karamar hukumar ta bada.”
“Tuni dai aka kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike,” a cewar Okoye.
