September 19, 2026

Rundunar Yan Sandan Jihar Kwara Ta Tabbatar Da Kashe Insfekta Da Garkuwa Da Dan Kasar China.

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da kashe wani insufektan yan sanda, Adebayo Adeforiti dake aiki da sashen yan sandan kwantar da tarzoma ta 15 dake Ilorin, wanda ke aikin gadi a kamfanin gine-gine na CGC dake kan hanyar Shao/Oloru, hadi da sace wani dan kasar China dake aiki a yankin. Ana dai da zargin cewa masu garkuwa da mutane ne suka tsere zuwa cikin daji da su.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa manema labarai a Ilorin babban birnin jihar Kwara.

Bayan faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Talata Assayomo ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi, domin ceto tare da cafke masu aikata laifukan.

Sai dai ya shawarci al’ummar jihar da su kula, su kuma bai wa ‘yan sanda duk wani bayani da zai taimaka wajen samun nasarar aikin su, inji majiyar Popular News Hausa ta AIT.

Kwamishinan ya kuma jajantawa iyalan insefekton na ‘yan sandan da ya rasu da ɗan kasar China da aka sace, inda ya yi alkawarin cewa ba wanda za a kyale ba a hukunta ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *