September 17, 2026

An kama masu safarar karuwai ga ‘yan fashin daji

0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 26 da take zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da mata huɗu da ake zargi suna aiki tare da wani gawurtaccen ɗan fashin daji a Jihar Kaduna.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ofishin rundunar gaggawa ta IRT ranar Talata, kakakin rundunar ta ƙasa Frank Mba ya ce matan da kuma wani namiji na yi wa ‘yan fashin safarar karuwai zuwa cikin daji.

Ya bayyana sunayen matan da; Maryam Abubakar, Lawisa Hassan, Jummai Ibrahim, Hajara Abubakar. Sai kuma namijin mai suna Muslim Mohammed.

Kazalika suna tattara wa wani shugaban ‘yan fashi bayanan sirri da aka bayyana da suna Isah Ibrahim, a cewar Mista Mba.

Bugu da ƙari, ‘yan sandan sun kama wani matashi mai shekara 24 da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro mai shekara tara kuma ya karɓi kuɗin fansa a wajen mahaifansa naira miliyan ɗaya da rabi a Abuja.

Rahoton BBC

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *