An Bada Dubban Kayan Jin Kai Ga Yan Gudun Hijirar Boko Haram A Najeriya.
Hukumar bunkasa yankin arewa maso gabacin Najeriya ta mika buhunan kayan abinci 10,000 da sauran kayan sanwa ga mutanen da ta’addancin yan Boko Haram ya shafa don ganin sun samu saukin rayuwa.
Akwai dai tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram kimanin 60,000 da iyalan su da yanzu haka suke masu gyaran hali a wasu cibiyoyi dake jihar Barno.
Shugaban hukumar Mohammed Alkali ya ce, an bada kayan tallafin ne domin taimaka ma gwamnatin jihar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin tattaunawa tsakanin hukumomi don maida mutanen a matsugunnansu na sali.
Alkali ya ce hukumar ta samar da kayan abincin ne daga wani kamfanin abinci, a kokarinta na farfado da masana’antun yankin.
Da take amsar kayan a madadin gwamnatin jihar Borno, shugabar hukumar bada agajin gaggawar jihar Hajiya Yabawa Kola ta gode ma hukumar bisa bada kayan agajin, tare da ba hukumar tabbacin gwamnatin jihar na dawo da zaman lafiya.
Kayan da aka bada sun hada buhunan shinkafa dubu 10, buhunan masara dubu 10, katon din sufageti dubu 4, galon nadin man sanwa dubu 4, barguna dubu 5, da kuma tabarmin roba dubu 5.
