September 19, 2026

An Ja Kunnen Manoma A Mani Da Cewa Kada Su Shuka Amfanin Gona Mai Tsawo.

0

An ja kunnen manoma a karamar hukumar Mani da su guji yin shuka mai tsawo kusa da hedkwatar karamar hukumar don guje ma ba yan ta’adda mafaka.

Durbin Katsina Hakimin Mani Umar Babani Isa ya yi wannan jan kunnen a lokacin da yake yin taro da magaddanshi.

Ya kuma umarci magaddan da su wayar da mutanensu su shuka kayan gona marasa tsawo da ba zasu hana a hango muggai ba idan sun shiga yankin.

Ya hori mutane da su guji dabi’ar nan ta sakin dabbobinsu su yi ta yawo cikin gonakai da kuma kan hanya, inda ya ce duk wanda aka kama yana yin hakan zai gane kuranshi.

Hakimin ya kuma tunatar magaddan buƙatar dake akwai ta daukar mataki akan sabbin fuska, masamman ma Fulani makiyaya don ganin an magance fada tsakaninsu da manoma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *