Kwamishinan Yan Sandan Adamawa Ya Yi Allawadai Da Wata Cakusa Tsakanin Yan Sanda Da Sojoji.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, Sikiru Akande, ya yi Allah-wadai da rikicin da ya barke tsakanin ‘yan sanda da sojoji a hanyar Numan a jihar.
Rikicin ya haifar da musayar wuta da kashe jami’in soji da ke bakin aiki.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje ya fitar, ya ce kwamishinan yan sandan ya bayar da umarnin cafke ‘yan sandan da ke da hannu ciki, tare da gudanar da cikakken bincike kan lamarin da nufin tabbatar da zaman lafiya da adalci.
Kwamishinan yan sandan ya yi gargadin cewa ba za a sake lamuntar kai hari kan jami’an tsaro da ke bakin aikinsu ba ta kowace irin salo, domin rundunar ta dauki nauyin rayukan dukkan jami’an tsaro, kuma za a dauki mataki ga irin wannan matsalar yadda kamar yadda doka ta tanada.
Hakazalika ya nanata kudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyi tare da jaddada cewa yana da matukar muhimmanci a hada kai da sauran jami’an tsaro wajen kare hakkin jami’an tsaro, domin ba su damar ci gaba da aikinsu.
Kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira da a kwantar da hankula saboda manyan jami’an tsaron biyu na yin duk mai yiwuwa bisa doka don ganin an shawo kan lamarin.
