SUBEB Da BESDA Na Horas Da Malamai Akan Tattara Bayanai A Zamance A Katsina.
Auwal Isah
Hukumar bada ilimin bai daya ta Jihar Katsina SUBEB hadin gwiwa da shirin samar da ingantaccen ilimi BESDA sun shirya taron horas da malamai na kwana 2 akan tattara bayanan dalibai a zamanace a jiya Talata 17 zuwa yau Laraba 18 ga wannan watan da muke ciki.
Horan na gudana ne a dakin taro mai suna “Conference Hall of Education Resource Centre Katsina”.
Da yake bude taron, shugaban hukumar bada ilimin bai daya ta jihar Katsina wato SUBEB Lawal Buhari Daura, ya ce bada horon nada nufin horas da malamai akan amfani da fasahohin zamani wurin tattara bayanan dalibai.
Shugaban hukumar bada ilimin bai dayan da ya samu wakilcin sakataren hukumar Dr. Isah Idris Zakari, ya bayyana shirin bada horon a matsayin abu mai amfani da ya zo kan kari ga masu daukar horon.
Kamar yadda ya bayyana, gwamnatin jihar Katsina ta hanyar ma’aikatar ilimi da hukumar SUBEB ta na sahun gaba wurin haras da ma’aikata.
Alhaji Lawal Buhari Daura ya yi kira ga mahalarta horon da su maida hankali akan abinda ake koya masu, tare da yin amfani da shi a wuraren ayyukansu.
Ya kara da cewa, amfani da fasahar zamani wurin aje bayanai zai rage masu wahalhalun da suke sha wurin yin rijista a cikin aji.
Daga nan sai ya yaba ma gwamnatin jihar Katsina, da hukumomin bada agaji, dama sauran masu ruwa da tsaki wurin inganta ilimi tun daga tushe.
A jawabinshi na maraba, daraktan sashen bincike da kididdiga na hukumar SUBEB Muhammad Lawal Kofar Sauri, ya ce mahalarta horon 43 an zabo su ne daga kananan hukumomi 13 na shiyoyin jihar nan 3.
Ya ce babbar manufar bada horon ita ce, a rage yawan yaran da basu zuwa makaranta.
A nashi bangaren, wakilin hukumar bada ilimin bai daya ta kasa Mr. Moses Oyishe, ya ce hukumar na yin bakin kokarinta wurin rage yawan yaran da basu zuwa makaranta, tare da tabbatar dalibai masamman yaya mmata sun ci gaba da makaranta.
Sauran da suka halarci wurin sun hada darakatan wayar da kan jama’a Ahmad Sa’idu, da jami’ar hukumar bada ilimin bai daya ta kasa a jihar nan Hajiya Maryam Audi Kankara, da daraktan mulki na hukumar SUBEB Mustapha Babi, da dai sauransu.
