November 18, 2026

Ƙungiyar Marayu Ta Raba Masu Kayan Abinci A Ɗanmusa.

0

Daga Auwal Isah

Wata ƙungiya mai rajin tallafawa marayu (Orphans Charity Foundation Danmusa) ta raba wa marayu 78 kayan abinci a yankin.

Shugaban ƙungiyar Mai Unguwa Ibrahim Baballe ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar rabon kayan, wanda ya gudana a gidan margayi hakimin Ɗanmusa.

Kamar yadda shugaban ƙungiyar ya ce, samar da tallafin nada nufin sauƙaƙa masu rayuwa don ganin sun gudanar da azumin Ramadan da iyalansu cikin daɗi.

Malam Mai Unguwa Ibrahim Baballe ya kuma bayyana cewa, an zaɓo waɗanda suka amfana daga gidaje 15 waɗanda suka haɗa da maza 38 da mata 40.

Tun da farko da yake jawabi, sakataren ƙungiyar malam Hamza Tukur Ɗanmusa ya bayyana cewa, an kafa ƙungiyar ne da nufin taimaka ma marayu, musamman ma a bangare ilimi da kuma ciyarwa domin inganta rayuwarsu.

Malam hamza Ɗanmusa ya ƙara da cewa, ƙungiyar tana gudanar da aikace-aikacenta ta hanyar amfani da gudumuwar da ƴaƴan ƙungiyar ke bayarwa, da kuma wasu daga cikin ɗaiɗaikun mutane.

Ya kuma yaba ma gudunmuwar da Dattijon ƙungiyar Mamman Abubakar Ɗanmusa, da hakimin Ɗanmusa, da kuma sauran iyayen kungiyar suke bayarwa wanda shi ne ya kai ƙungiyar ga nasarori.

Shima da yake jawabi, mataimakin shugaban ƙungiyar Mai-unguwa Alhaji Lawal Ɗantiye ya yi amfani da damar bakin wajen yin kira ga alumma da su cigaba da yin addu’o’i musamman a cikin wannan watan na Ramadan domin neman ɗauki wajen Allah don ganin matsalar tsaron da ake fama da ita ta zo karshe.

Ya yi bayanin cewa, ƙofa a buɗe ta ke ga duk wanda ke da buƙatar bayar da gudumuwarshi ga ƙungiyar ta hanyar tuntubar kungiyar kai tsaye ko kuma ta lambar asusun ajiya na bankin kungiyar.

Mai Unguwa Alhaji Lawal Ɗantiye ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da suyi kyakyawan amfani da shi yadda ya kamata.

Wasu daga cikin waɗanda suka samu tallafin sun nuna jindaɗinsu tare da bayar da tabbacin yin kyakyawan amfani da kayan yadda ya kamata.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *