Katsina City News Za Su Shirya Taron Tattaunawa Da Masu Sha’awar Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Katsina
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Sanannan dandalin sada zumunta na whatapp mai suna Katsina City News zai shirya wani taron tattaunawa tsakanin masu neman tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina wanda ake sa ran kowa zai gabatar da manufofi da kudirorinsa da kuma shirin da yake da shi idan ya samu nasara.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata nasarwa da mamalakin shafin Katsina City News Ɗanjuma Katsina ya sanyawa hannu kuma ya rabawa manema labarai ciki harda Popular News Hausa
Sanarwar ta ce maƙasudin shirya wannan tattaunawa ya biyo bayan shawarar da Alhaji Ibrahim Ahmad Daku (Sanyinnan Katsina) wanda kuma ya samu goyon bayan Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro da kuma
Alhaji Sada Salisu Ruma da sauran mambobin shafin whatapp na Katsina City News suka bada
Ta ƙara cewa dandalin ya amince a shirya wannan taron tattaunawa wanda kuma tuni aka kafa wani kwamiti da zai shirya taron wanda kuma za a watsa shi kai tsaye ta kafafen sada zumunta daban-daban na zamani.
Mambobi 21 da aka zaɓa daga ɓangarori daban-daban da suka haɗa da ‘yan siyasa da kungiyoyin da ba na siyasa ba, da wakilan kungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki da dattawa da sanannun mutane da sauran jama’a.
Haka kuma wannan kwamiti zai fitar da tsarin da za a gudanar da wannan tattaunawa wanda za a sanar da waɗanda abin shafa da zaran an kammala shirye shirye.
Ƙwamitin shirya taron tattaunawa da masu sha’awar tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina kuma mambobi ne daga dandalin sada zumunta na whatapp na Katsina City News na 1 da na 2 da kuma na 3
Waɗannan su ne mambobin kwamitin na mutum 21
Alhaji Ibrahim A Daku, Chairman
Alhaji lawal Rufai Safana
Alhaji Ibrahim Katsina
Barista Ahmad Danbaba
Alhaji Sada Salisu Ruma
Chairman, ASUU UMYU Chapter.
Chairman, Network for Justice, Katsina, Alhaji Dauda Kurfi
Eng Kabir Hussein (Jakadan Ruma)
Zainab Hamza
Zainab Shittu
Haj. Murja Saulawa
Haruna Shittu Gozaki
Ismail Adamu
Jamilu ismaila Mabai
Lawal Adamu Shunku.
Ibrahim Bature
Bashir Danjuma
Sheikh Abu ammar
Sheikh Ibrahim iyal Gafai
