Gudun Tsira Da Rai: Mutane Bakwai Sun Rasu Saboda Tsoron Harin ‘Yan Bindiga A Katsina
Al’ummar kauyen Shimfida da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina na cikin mawuyacin hali sakamakon rashin jami’an tsaron da za su basu kariya domin gudanar da lamurransu na yau da kullum.
Wasu mazauna garin sun shaida wa wakilinmu cewa, a safiyar ranar Alhamis 10 ga watan Maris, 2022, da misalin karfe 10 zuwa 12 na safe, wasu motocin sojojin Najeriya, sun shiga garin suna kokarin kwashe jami’an tsaron garin domin yin kaura zuwa wani sansani daban.
Jim kadan bayan tabbatar da cewa sojojin za su yi balaguron da babu dawowa ne, jama’a suka tattara kayansu na amfanin yau da kullun suka fara gudun tsira.
Yayin da suke kokarin neman mafaka, ‘yan bindigar sun yi nasarar yin garkuwa da wasu daga cikin mutanen kauyen, yayin da suka jefa harsashi a cikin dandazon ‘yan gudun hijirar.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai maza da mata, an yi jana’izarsu ne a masallacin Juma’a na Hamza Bin Abdulmudallib da ke Tudun Wada Jibia, a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
