Gurbataccen man Fetur: Kamfanin Duke dana Oando sun ce mansu ya cika sharuddan Najeriya.
A jiya ne Kamfanin mai na Duke da Oando suka karyata zargin da ake yi masu na shigowa da gurbataccen mai a cikin kasar nan kwanan nan.
Kamfanonin biyu yayin da suka bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur (Downstream) da ke binciken halin da ake ciki, sun ce man nasu ya cika sharuddan da Najeriya ke bukata.
Manajan Daraktan Kamfanin na Duke Oil, Lawal Sade a cikin jawabinsa a gaban kwamitin ya bayyana cewa, kayayyakin da kamfaninsa ya shigo da su, sun tabbatar da ingancinsu a tashar lodin kaya da kuma tashar jiragen ruwa daga hukumomin da abin ya shafa.
Sai dai ya ce kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya sanar da su cewa, man na dauke da wasu sinadarai da suka gurbata shi.
“Duke Oil kamfani ne na kasuwanci na kasa da kasa da ke sana’ar man fetur dama danyen mai.
Ya kuma ce tuni aka kebe wannan man.
Madogara: leadership newspaper
